An shiga rudani a karshen mako yayinda fustattun al’ummar unguwa suka kama wata mata da ake zargi da Shanye Jinin wani yaro har ya mutu a yankin Hotoro Filin Lazio dake Kano.
Hakan na zuwa ne yayinda Labarai makamantan wannan na shanye Jinin mutane da zarar wasu mata sun shiga gidaje sun bukaci a basu ruwan sha ke cigaba da ruruwa a sassa daban-daban na Arewa maso yammacin Najeriya.
Wakilinmu, Rabiu Usman ya tuntubi Mahaifin yaron da ake zargi an shanyewa Jini ya mutu, Mai Suna Nura Nafiu, inda ya musanta hakan yana mai cewa sun garzaya Asibiti da yaron Kuma ance zazzabin cizon sauro ne ya sameshi.