Shugaban Kwalejin Fasahar sarrafa Amfanin Gona ta tarayya dake jihar Kano, Dr Muhammad Yusha’u Gwaram, ya bayyana aikin noma a matsayin ingantacciyar hanya wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Dr Gwaram ya bayyana haka ne yayin da a karon farko kwalejin ta gudanar da bikin rantsar da sabbin dalibai da za su yi karatu a fannoni daban-daban na kwalejin.
Kazalika Ya yi gargadin cewa kwalejin da su maida hankali a karatunsu domin zama ‘yan kasa da zasu jagoraci samar da sauyi da dogaro da kai da wadata Najeiya da Abinci.
Da take zantawa da wakilinmu Kamaluddeen Mohammad darakta sashin tuntuba a kwalejin, Hajiya Aishatu Maiwada Ahmad, ta bayyana cewa kimanin Dalibai 200 akayi bikin rantsarwa, tana mai jaddada cewa kwalejin ta bullo da tsarin karatu na wurin gadi nufin karfafa gwiwar masu sha’awar aikin gona.
Hajiya Aisha Maiwada Ahmad ta kuma gargadi daliban da su nisanta kansu daga kungiyoyin asiri da sauran nau'o'in laifuka dake barazana ga zamantakewar jama'a saboda makarantar ba za ta amince da kowane nau'i rashin ‘Da’a ba.
Shima, Babban daraktan cibiyar wayar da kan jama’a da rashin tabbatar da adalci, CAJA Comrade Kabiru Sa’idu Dakata ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar cin zarafi a manyan makarantu, sai dai ya dora alhakin wasu matsalolin akan dalibai da ke gayyatar cin zarafi.
Ya bukaci daliban da su kai rahoton duk wani cin zarafi yana mai kira ga daliban suma su rika sanya tufafin da suka dace, yayinda ya yabawa hukumar kwalejin ta aikin gona bisa daukar matakan da suka dace da kuma shirya bikin rantsar da daliban na farko.