On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Zargin Zagon Kasa: Kwankwaso Na Fuskantar Barazana A Jam'iyyar NNPP

Shugabannin jam’iyyar NNPP a Najeriya sun bukaci dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso  ya yi murabus ba tare da bata lokaci ba ko kuma a dakatar da shi har sai baba ta gani a kan wasu zarge-zarge na yiwa jam’iyyar zagon kasa.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Sunday Oginni ya fitar, ya bukaci Kwankwaso ya yi karin haske game da dangantakarsa da jam’iyyar APC a lokacin zabe da kuma bayan kammala zabukan 2023.

Oginni ya nuna bacin ransa akan yadda Kwakwaso ke yawan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya zargi tsohon gwamnan da kitsa rikicin NNPP domin  kwace ikon  jam’iyyar tare da nemawa kansa mafita a fagen siyasar Najeriya.

Ya ce ya gano cewa Kwankwaso tare da hadin gwiwar wadanda yake aiki da su sun yiwa kundin tsarin mulkin jam’iyyar kwaskwarima domin yin garkuwa da tsarin jam’iyyar.

Har yanzu bangaren Kwankwaso bai mayar da martani kan zargin ba.