Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zai yi ritaya zuwa mahaifarsa da ke Daura a jihar Katsina domin ya huta kuma ya yi nisa da Villa domin gujewa matsaloli idan ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu na shekarar 2023.
Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin mazauna Abuja dake bikin Kirsimeti a jiya, ya nuna godiya ga ‘yan Najeriya da suka ba shi damar zama shugabansu.
Ya sake yin alkawarin cewa ba zai kara ko kwana daya a fadar mulki bad a zarar wa’adinsa ya cika.
Tunda farko a sakonsa na Kirsimeti, shugaba Buhari ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa masu neman kawo cikas ga zaman lafiya a kasarnan sunyi rashin nasara.
Ya kuma jaddada cewa Alheri mai yawa yana jiran Najeriya a shekarar 2023 da bayanta.
Yayi fatan zaman lafiya da farin ciki da suka mamaye wannan lokaci zasu cigaba da wanzuwa har zuwa sabuwar shekara da zabuka a watan Fabrairu da kuma bayan lokutan.
Yayin da yake yi wa daukacin ‘yan kasa mabiya addinin Kirista barka da Kirsimeti, Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna soyayya da kulawa da kuma tausayawa juna.