‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da ke addabar kasarnan idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa na III a fadarsa da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.
Yace ziyarar ga sarkin ta zama wajibi saboda girmama masarautun gargajiya da daukacin mutanen garin Keffi.
Da yake yabawa Kwankwaso bisa ziyarar, Sarkin Yamusa na III ya yi masa fatan Alheri.