Wasu ‘yan bindiga sun sake kai farmaki unguwar Gandu tare da yin garkuwa da wasu dalibai a jami’ar tarayya da ke Lafia.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, da farko ‘yan bindigar kai harin cikin ayari da karfe 7:30 na Almuru a ranar Laraba, amma sai suka gudu suka shiga daji domin buya na tsawon sa’o’i da dama bayan da suka lura da jami’an tsaro.
Sun sake tasowa da tsakar daren ranar alhamis daura da ginin jami’ar, inda suka kwashe kimanin sa’o’i uku suna gudanar da ayyukansu cikin walwala, daga bisani suka yi awon gaba da dalibai biyar a yayin da da dama suka samu raunuka.
Da yake tabbatar da faruwar al'amarin, kakakin jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya ce har yanzu ba a tantance adadin daliban da aka sace ba amma ya ce dalibai uku ne zuwa biyar.
A wani bangaren kuwa, daliban jami'ar ta Lafiya dake Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Alhamis, inda suka bukaci a kawo karshen yawaitar harin garkuwa da dalibai da ake yi a yankin.
Rahotanni sunce an sace dalibai sama da 15 na jami’ar a wannan zangon karatu tare da biyan makudan kudin fansa a cikin mawuyacin hali.
Daya daga cikin wadanda harin da aka kai a baya ya rutsa da su, ya shaida wa jaridar daily trust cewa ‘yan bindigar sun lakadawa biyar daga cikin su da aka yi garkuwa da su duka tare da yi musu barazana a cikin dare har wayewar gari.
Wanda abin ya shafa ya kara da cewa daga baya sun karbi Naira dubu 500 daga hannun iyayensa suka sake shi, yayin da bai san abin da ya faru da sauran ba saboda ba za su iya biya ba.