Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed, ta musanta zargin da ake yi cewa tayi cushe a kasafin kudin wasu ma’aikatu da hukumomin Najeriya
Ministar, wadda ta ce gwamnatin tarayya ta dauki matakin tabbatar da gaskiya da tafiya da komai bude a cikin tsarin kasafin kudi, ta kuma bayyana cewa anyi kuskuren shigar da adadin kudaden da ake magana a kai ne cikin kididdigar kasafin kudin da aka mikawa Majalisar Dokoki ta kasa.
Idan ba a manta ba ministar ma’aikatar jin kai ta yi zargin cewa bata da masani akan kudi naira billiyan 206 da milliyan 242 da dabu 395 dake cikin kasafin kudinta.
Sai dai mai ba da shawara na musamman ga ministar kudi kan harkokin yada labarai Yunusa Tanko Abdullahi, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, yace anyi kuskuren shigar da adadin kudaden ne a kididdigar kasafin kudin da aka mikawa majalisar dokoki ta kasa.
Shi kuwa kwamitin da ke kula da harkokin al’umma na majalisar dattawa ya bankado yadda ake zargin anyi sa hannu na bogi wajen biyan sama da Naira miliyan 208 ga wadanda suka ci gajiyar shirin koyon sana’o’i na wata shiyya.
Ma’aikatar kwadago da ayyukan yi itace ta shirya horon a dukkan shiyyoyin kasar nan guda shida a shekarar 2021, inda aka ware Naira miliyan 35 ga kowacce shiyya banda Kudu maso Gabas, da ta samu Naira miliyan 32.
Haka kuma Majalisar dattijai tana binciken sama da hukumomin gwamnati 200 da suka ci gajiyar Naira tiriliyan 5 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021.
Kwamitin da Sanata Matthew Urhoghide ya jagoranta ya sha alwashin daukar matakan da suka dace akan wanda aka samu da hannu.