On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Zamu Yaki Kwacen Waya Da Sauran Laifukan Ta'danci A Kano - Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda

Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano Abubakar Lawan ya sha alwashin yaki da matsalolin kwacen waya da sauran muggan laifuka ta hanyar shirin wanzar da zaman lafiya.

Da yake jawabinsa na farko ga al'umma da kum a jami'an, kwamishinan 'yan sandan ya ce tuni ya zauna da manyan jami'an 'yan sanda da turawan 'yan sandan domin labubo hanyoyin magance aikata laifuka a faɗin jihar Kano.

Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya ya rawaito CP Lawan ya ƙara da cewa tuni sun ɗauki matakin wanzar da zaman lafiya a jahar Kano ( Operation Restore Peace) dan yaƙi da masu Ƙwacen waya da kuma Ƴan Daba, ta hanyar sauya tsarin nan na kan kace kwabo wato Operation Puff Adder .

" Mun kawo tsare-tsare a harkar gudanar da tsaro na yin aiki tsaro da al'umma da kuma wayar da kansu a kafafan yaɗa labarai da shafukan sada zumunta ".

Kazalika kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Abubakar Lawan ya ce za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da suka haɗa da Sojojin ƙasa, Sojojin sama, DSS  , Civil Defence,kwastam, Immigration, FRSC , Karota, da kuma jami'an Bijilanti da sauran ƙungiyoyin tsaron yan sakai.

" Za kuma mu yi aiki da Malamai, Sarakuna, ƙungiyoyi masu zaman kansu da na PCRC , Yan jaridu da ƙungiyoyin matasa domin tabbatar da tsaro da haɗin kai a jahar Kano.

Haka kuma kwamishinan ya godewa gwamnati da  al'ummar jahar Kano da irin addu'o'in da suke yi a koda yaushe .