On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Zamu Tallafawa Mata 4,400 Daga Kananan Hukumomi 44 - Gwamnatin Kano

A wani shiri na inganta tattalin arzikin Mata da ci gaban su, gwamnatin jihar Kano ta ce zata tallafawa Mata dubu hudu da dari hudu; Mata ɗari-ɗari daga kowacce ƙaramar hukuma a cikin wannan watan na Maris.

Da yake jawabi  a yayin karɓar bakuncin Mata karkashin jagorancin ƙungiyar Sasanta rikice-rikice da sanar da cigaba,  a wani bangare na shirye-shiryen bikin ranar mata ta duniya, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jiha, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya wakilta, ya ce   gwamnatin Kano za ta cigaba da baiwa mata dama a fannin ilimi da bunkasar tattalin arzikinsu. 

A zantawarta  da wakilinmu Kamaluddeen Muhammad, wacce ta wakilci Matan Jamila Musa ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kara haɓaka fannin ilimin Mata da karfafa tattalin arzikinsu da nufin bunkasar cigaban ƙasa baki daya.

Jamila ta yi nuni da cewa, za a iya samun hakan ne ta hanyar aiwatar da manufofi da tsare-tsare na inganta ilimin Mata, da tabbatar da samar da daidaito a ayyukan yi da sauran su. 

Shima Babban daraktan shirin sasanta rikice-rikice da kawo cigaba Dr Muhammad Mustapha Yahaya, Yayi kira ga gwamnatin data  baiwa kungiyoyin fararen hula damar a dama dasu wajen yin tsare-tsaren cigaban al'umma.
Ana bikin ranar Mata ta duniya duk ranar 8 ga Maris.