Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa ta tsara wasu kudurori guda goma sha daya domin zama jagora wajen aiwatar da manufofinta da shirye-shiryenta.
Da yake jawabi a wajen taron sanin makamar aiki na kwana biyu da ofishin sakataren gwamnatin jihar ya shiryawa mambobin majalisar zartarwa, Gwamna Mai Mala Buni, ya ce manufar gwamnatinsa ita ce samar da hadin kai tsakanin ma’aikatu da hadin gwiwa wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare guda 11. .
Ya kuma yi nuni da cewa daga cikin manufofin akwai karfafa hadin gwiwar tsaro na cikin gida sai ilimi da kiwon lafiya da noma da kasuwanci da masana’antu tare da kammala fitattun kasuwanni a garuruwan Potiskum da Geidam yayin da za’a kammala tashar motocin tirela a Potiskum.
Sauran sun hada da ababen more rayuwa da gidaje da albarkatun ruwa da muhalli da samar da kafofin arziki da rage radadin talauci da gudanar da mulki a bude da doka da oda.
A nasa jawabin, sakataren gwamnatin jihar Yobe, Baba Mallam Wali, ya ce taron na karawa juna sani da sabbin kwamishinoni kan ginshikan gwamnatin Mai Mala Buni na jihar Yobe, tare hangen nesa kan abubuwan da suka sa a gaba, da tabbatar da shugabanci nagari da sauransu.
Cikin mahalarta horon akwai Abdullahi Bego kwamishinan harkokin cikin gida da yada labarai da kuma raya al'adu da Mairo Ahamed Amshi kwamishiniyar ma'aikatar jin kai da kuma Kole Shattima dake baiwa gwamna shawara kan tsare-tsare da kuma sauran 'yan majalissar zartaswa.