Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana zaman lafiya a matsayin wani muhimmin al'amari na samun ci gaba mai ma'ana a Najeriya.
Daraktan kula da harkokin yada labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Olusola Abiola, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce mataimakin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi wata tawaga daga Masarautar Hadeija dake jihar Jigawa.
Shettima ya shaida wa tawagar da Sarkin Hadeja kuma Shugaban Majalisar sarakunan jihar Jigawa Alhaji Adamu Maje ya jagoranta cewa jihohin Kano da Jigawa suna morewa zaman lafiya.
Mataimakin shugaban kasar ya yabawa masarautar kan ci gaban da ta samu.
Dangane da matsalar ambaliyar ruwa da ake fama da ita a Jigawa, mataimakin shugaban kasar ya ce nan bada dadewa ba Gwamnatin Tarayya zata magance kalubalen saboda mummunan tasirin da takeyi a harkar noma da samar da abinci.