Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC), reshen jihar Kano ta bukaci gwamnatin Kano ta nemi amincewar majalissar dokokin jihar domin nemo sabon rancen kudi da zata biya hakokin ma’aikata da suka yi ritaya.
Kungiyar ta NLC reshen jihar Kano ta bayyana yunkurin gwamnatin Kano na kashe kudi Naira billiyan 10 wajen sayen Kyamarorin Tsaro a matsayin rashin fifita abunda ya fi muhimmanci.
NLC ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta aikowa Arewa Radio dauke da sahannun shugaban ta Comrade Kabiru Ado Minjibir da Sakatarensa Comrade Husaini Buddah.
Minjibir na da ra’ayin cewa maimakon yunkurin, kamata yi gwamnatin tayi amfani da rancen kudin wajen biyan ‘yan Fansho kudaden da suke binta, wanda ya kai Naira billiyan 27.
Haka kuma Kabiru Ado Minjibir ya roki gwamnatin Kano da ta hada kai da Majalissar dokoki domin sake Ranto wasu kudaden da zatayi amfani da su wajen biyan bashin kudaden Gratuti da sauran hakkokin Ma’aikata da suka yi Ritaya.