Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, ya dauki wani sabon salo, yayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gana da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers da wasu gwamnonin PDP a birnin Landan a daren ranara talata.
An sanar da manema labarai cewa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, da takwaransa na Jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, da sauran jiga-jigan PDP masu biyayya ga Wike sun halarci taron.
A ranara talata jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamna Wike da wasu abokansa sun fita kasar waje domin wani taron da aka bayyana a matsayin muhimmi kan makomar siyasarsu.
Gwamna Wike dai ya sha fama da yakin cacar baki da jam’iyyar sa kan kayen da ya sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP da kuma yadda kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zabi abokin takararsa.