Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta shawarci dukkanin jam’iyyun siyasa da su dage taron gangamin da suka shirya gudanarwa a yau Alhamis zuwa wani lokaci bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
A wata wasika da aka aike wa shugabannin jam’iyyun siyasa mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula ayyuka, DCP Mua’zu U Mohammed a madadin kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci jam’iyyun siyasar da mabiyansu da su bi shawarwarin domin samun maslaha da zaman lafiya.
A wasiƙar mai kwanan watan laraba 22 ga Fabrairu, 2023, rundunar ta ce jam'iyyun siyasa uku APC da NNPP da PDP sun sanar da rundunar gangamin da suka shirya gudanarwa yau Alhamis a birnin Kano
Cikin wani sakon murya da kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, yace bisa la’akari da yanayin tsaro da ake fama da shi a Jihar Kano da kasa baki daya,kwamishinan ‘yan sanda ya kira wakilan jam’iyyun siyasar uku zuwa wani taron gaggawa domin a samo bakin zaren da warware matsalar.
Rundunar ‘yan sandan ta koka da cewa, babu wata hanyar da za’a bi wajen gudanar da gangamin, inda ta yi kira ga dukkan bangarorin da su sauya ranar da kuma lokacin gangamin.