Kotun koli ta shirya zama ranar Alhamis domin tattaunawa kan karar da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya shigar, bayan da kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wadda ta soke nasarar da ya samu a zaben 2023.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya tabbatar da sanya ranar zaman sauraron karar da aka shirya, wanda ke da matukar tasiri ga makomar kujerar gwamnan jihar Kano.
Idan za’a iya tunawa kotun karrakin zabe da kotun daukaka kara sun amince da Nasiru Gawuna, dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben 2023.
Zaman kotun koli da ake shirin yi ya kara zafafa fatan bangarorin dake cikin shari’ar yayin da masu ruwa da tsaki ke dakon hukuncin karshe da zai tabbatar da wanda ya cancanta a matsayin gwamnan jihar Kano.