Kotun karbar kararrakin zaben gwamnan dake zamanta a Jihar Kano bisa jagorancin mai shari'a Justice Akintan Osadabay ta cigaba da sauraron karar da Jam'iyyar APC ta shigar dake kalubalantan zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023 da ya gabata.
Sai dai a zaman Kotun na ranar alhamis 20 ga watan Yuli 2023 da aka tsara domin wanda ake kara na farko hukumar zabe me zaman kanta ta Kasa INEC ta fara gabatar da shaidar kariya, Lauyan hukumar zaben Barista Oshayomi Emmanuel ya bayyanawa Kotun cewa ba su da wata shaida da za su gabatar gaban Kotun, dan haka suka rufe kariya gaban Kotun.
Lauyan Abba Kabir Yusuf R A Lawal SAN da kuma lauyan jam’iyyar NNPP John Olusola SAN ba su kalubalanci INEC ba akan rufe kariyar ta su.
Bisa hakan ne Justice Akintan Osadebay ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar Juma'a 21 ga watan Yuli 2023 domin baiwa wanda ake kara na biyu Injiniya Abba Kabir Yusuf damar fara gabatar da nasa shaidun na kariya a gaban Kotun.