Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa Jami’an tsaro da shugabannin rundunar ‘yan sandan Najeriya cewa al’ummar duniya na kallonsu.
Buhari ya ce mutane da dama na da kyakkyawan fata, inda ya bukace su da su samar da isasshen tsaro wajen tabbatar da gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Shugaban yayi wannan gargadin ne a shalkwatar rundunar da ke Abuja, yayin da yake kaddamar da muhimman kayyakin aiki da rundunar ta sayo.
Daga bisani shugaban ya ci gaba da kaddamar da kayayyaki daban-daban domin inganta ayyukan rundunar ta hanyar dabarun aiki, musamman a fannin kula da jama'a da kuma ayyukan dakile tarzoma.
Yace, samar da kayan aikin nada nufin inganta karfin ‘yan sanda domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro dukkan goyon bayan da suke bukata domin rubanya hazakarsu wajen tabbatar da tsaron kasarnan yadda ya kamata.
Wasu daga cikin kayan aikin sun hada da motocin aiki guda 127 sai makamai da alburusai ga jami’an hana tarzoma da hayaki mai sa hawaye da riguna masu sulke da sauran kayan kariya.