
Zababben shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa zababben shugaban kasa, Kashim Shetima sun karbi lambar girmamawa ta GCFR da GCON.
Daga yanzu za a rika kiran Tinubu da babban kwamandan Askarawan tarayyar Najeriya GCFR sai Shattima da ya zama mai lambar GCON.
A yayin bikin dake gudana a halin yanzu a babban birnin tarayya Abuja, za a mika kundin karbar mulki ga sabbin zababbun shugabannin.