Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya ce Lafiyarsa Kalau sannan kuma a shirye yake wajen tafiyar da harkokin mulkin kasar nan,Gabanin rantsar dashi a matsayin shugaban taraiyyar kasar nan.
Tinubu ya baiyana haka ne jim kadan bayan dawowarsa gida Najeriya bayan shafe kimanin wata daya yana hutu a birnin Paris na kasar Faransa.
A lokacin da yake yiwa manema Labarai jawabi a filin jirgin sama na Abuja, Tinubu ya musanta rahotannin dake cewar ya fita kasar nan ne domin a duba lafiyarsa saboda wata rashin lafiya da ba’a baiyana ba.
Dangane da tsare-tsaren da yake yiwa kasar nan kuwa,Tinubu ya ce a yanzu haka yana tattaunawa tare da neman shawara kan yadda za’a samu nagartacciyar gwamnati da zarar an rantsar dashi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan gobe.
Zababben shugaban kasar ya wallafa hotonsa a shafinsa na Tuwita inda ya baiyana cewar yana farin ciki da dawowarsa gida Najeriya.