Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin yin ‘kasa-‘kasa da dukkanin tutocin Najeriya a kasar nan da wadanda suke a ofisoshin jakadancin kasashen waje dake Najeriya a ranakun 11 da 12 ga watan Satumba domin girmamawa ga marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu data mutu a ranar Alhamis.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
An sanar da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu da yammacin ranar Alhamis.
Ita ce Sarauniyar Ingila da sauran kasashen renon ingila tun daga ranar 6 ga watan Fabrairun 1952, har zuwa shekarar 2022 lokacin data koma ga mahalicci.
Marigayiya Sarauniya Elizebeth ta Biyu
Ta shafe na shekaru 70 da kwanaki 214 tana sarautar Ingila, kuma itace wadda tafi dadewa akan sarautar Burtaniya.