Sufeton Rundunar Yansanda ta kasa, Usman Alkali Baba, Yace za’a tura jami’an yansanda dubu 21 domin tabbatar da tsaro a yayin zaben gwamnan jihar Osun, na ranar 16 ga watan da muke ciki da za’a yi.
Alkali wanda ya baiyana haka a birnin Osogbo yayin wani taron masu ruwa da tsaki, wanda Hukumar Zabe ta kasa, mai zaman kanta ta shirya, Yace ba’a tura jami’an yansandan domin cin zarafin jihar ba, sai dai kawai domin kawar da dukkanin wasu miyagun aiyuka da ka iya kawo cikas wajen gabatar da zaben.
Kazalika yace, jami’an yansandan zasu bayar da cikakken tsaro, tare da kare masu yin zabe da kuma kayan da za’a yi amfani dasu wajen yin zaben.
Bugu da kari, Sufeton rundunar yansandan ta kasa, Ya baiyana cewa jami’an tsaron da za’a tura sun samu horo na musamman sannan kuma sun san dokokin da gwamnati ta shimfida, sannan kuma ya bada tabbacin cewa jami’an yansandan zasu kauracewa tsoma kansu cikin harkokin siyasa.