Sabon shugaban Hukumar Kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano da aka fi sani da KAROTA, Injiniya Faisal Mahmud Kabir ya ce , za’a yiwa jami’an Hukumar sabon Kaki da kuma yin garan bawul kan yadda ake gudanar da aiyukan hukumar.
Shugaban ya baiyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an karota na musamman dake aikin sa kai a ofishinsa, a wata ziyarar bangirma da suka kai masa.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Nabilusi Abubakar Ya fitar a jiya.
Shugaban hukumar Karotar ya tabbatar da cewar zasu yi duk abunda ya dace bisa hurumin da suke dashi a dokance, domin kula da zirga-zirgar ababen hawa da kuma tsaftace yadda ake amfani da titinan jihar kano.