Hukumar bincike kan tafiyar da harkokin kudi cikin sirri a Najeriya NFIU ta ce za a rufe dukkannin asusun gwamnati a farkon watan Janairu a wani yunkuri na dakile sayen kuri’u a babban zaben 2023.
Hukumar ta ce za ta kyale iya kudaden da za su wadatar a biya albashin ma’aikata da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum na ma’aikatu, sassan da hukumomi.
Darakta Janar na hukumar NFIU Modibbo Turkur shi ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki na kwana daya da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya yi tir da illar sayen kuri’u ga zabukan Najeriya.
Ya ce galibin mutanen da ke sayen kuri’u suna yin haka ne saboda suna iya tasarrafi da kudade da ba na su ba, don haka akwai bukatar daukar mataki.