Majalisar wakila na wai yunkuri domin kara yawan tarar da ake ci kan wadanda aka samu da lefin wulakanta Tutar Najeriya daga naira 100 zuwa naira dubu 100.
A jiya ne kudirin yin gyara kan girmama Tutar Najeriya ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilan.
Dan majalisa Sada Soli na jam’iyyar APC daga jihar Katsina wanda ya gabatar da kudirin, ya ce ana samun daidaikun al’umma da kuma jama’ar gari da wasu kungiyoyin dake cikin wulakanta tutar Najeriyar.
Da yake yanke hukunci kan kudirin, Mataimakin shugaban majalsiar Benjamin Kalu ya mika kudirin gaban kwamitin majalisar daya da ce domin daukar mataki na gaba.