Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir, Ya baiyana aniyarsa na kawo karshen shirin nan dake bada tallafi wajen bunkasa ilimin ‘ya’ya mata mai suna AGILE a cikin jiharsa ta Katsina.
Sarkin ya baiyana cewar shirin ya saba da tanadin koyarwar addinin musulunci da kuma al’adun mutanen yankin arewa, wanda hakan ke zama wata makarkashiya ga iyaye da kuma al’ummar gari.
Ya ce ya zama wajibi a dauke shirin na AGILE daga jihar Katsina, kuma ba zai lamunci duk wani tsari da zai zama katsalandan ga tafarkin koyarwar ilimin da ake kanta a halin yanzu ba.
Idan ba’a manta ba, Koda a nan kano, wata kungiyar farar hula mai suna Kungiyar Matasan Kano, ta roki gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya kafa kwamitin bincike domin gano wasu zarge-zarge na boyayyiyar manufar dake shirin na AGILE, wanda yanzu haka ke gudana a wasu makarantu na jihar Kano domin yin gyaran da ya da ce.