A ranar Alhamis mai zuwa ce, Za’a karrama zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da lambar girmamawa ta kasa GCFR, da kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za’a bashi lambar girmamawa ta GCON.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai jagoranci bukin bada lambobin karramawar.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hadimin shugaban kasa ta bangaren kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi ya fitar.
Kazalika sanarwar ta baiyana cewar a ranar ne kuma za’a mika kundin bayanan mika mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.