‘Yan kasuwar man sun tabbatar da cewar da yuwuwar a sake samun tashin farashin man fetur a cikin watan nan, sakamakon faduwar darajar Naira a kan Dala da kuma hauhawar farashin danyen mai a duniya.
Duk da cewa Kamfanin Man fetur na kasa da sauran ‘yan kasuwar man ba su sanar da karin farashin man fetur din ba, sun tabbatar da cewa karancin kudin kasashen waje da hauhawar farashin danyen mai sune muhimman abubuwan da zasu sa a kara samun tashin farashinsa.
Shugaban Kungiyar na kasa,Billy Gillis-Harry, ya ce muddin darajar Naira zata cigaba da faduwa farashin man fetur zai ci gaba da karuwa.
Ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya farfado da matatun man kasar nan cikin gaggawa batare da bata lokaci ba.