On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Za'a Kafa Kotunan Tafi Da Gidanka Guda 200 Domin Hukunta Masu Karya Ka'idojin Hanya - FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar  hadurra ta kasa, ta ce ta kafa kotunan tafi-da-gidanka sama da 200 domin gurfanar da wadanda suka aikata laifukan tuki a yayin gudanar da aikin sintiri na musamman na bubukuwan  Easter a fadin kasarnan.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya ce kafa kotunan tafi-da-gidanka nada nufin  tabbatar da gudanar da bukukuwan Easter  na shekarar 2023 lami lafiya da kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa, shugaban hukumar, DaudaBiu, ya bukaci kwamandojin  hukumar da su tabbatar da an tura ma’aikata domin tabbatar da dokokin hanya.

Biu ya kuma bukace su da su tabbatar da kawar da duk wani cikas da kuma samar da saukin zirga-zirga a dukkan manyan titunan kasar nan.