Babban Sufetan ‘yan sandan kasar nan , Usman Alkali Baba ya bada da tabbacin yin hadin gwiwa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa domin gurfanar da masu aikata laifukan zabe har guda 781 da aka kama a zaben bana a fadin kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a lokacin ganawar sa da mu’kaddasan sifetan yan sanda da mataimakansa na shiyoyin rundunar a shalkwatar rundunar domin duba irin kwazon da rundunar tayi a yayin gudanar da zaben daya gabata
Baba ya kara da cewa an samu tarin kura-kurai har guda 489 da aikata a zaben da aka yi.
Ya kara da cewa, An basu umarnin mika takardun korafe-korafen da aka samu zuwa ga ofishinsa domin yin aiki tare da sashen shari’a na Hukumar zabe ta kasa INEC kan yadda za’a gurfanar da wadanda aka samu da lefi a gaban kotu.