Hukumar Kula da Yanayi ta kasa taja hankalin jama’ar jihar Kano da wasu jihohin na Arewacin kasar nan, dasu shirya fuskantar ruwan sama kamar dab akin kwarya nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, Ta baiyana cewar a yanzu haka ana fuskantar yawaitar cida da gajimare a wasu bangarori na Arewacin Najeriya, Cikinsu hadda nan jihar Kano da Borno da Jihar Taraba da Gombe da kuma jihar Bauchin Yakubu.
Hukumar kula da yanayin ta kasa, A wuraren da ake samun yawaitar cida, Za’a iya samun kadawar iska mai karfi kafin saukar ruwan sama ,wadda zata iya karya turakun wutar lantarki da Bishiyoyi da kuma gine-gine.
Kazalika hukumar ta ja kunnen jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da zama a cikin gidajensu musamman a lokacin da ake samun saukar ruwan sama mai karfe, domin kaucewar fuskantar tsawa.