Hukumar kula da yanayi ta kasa, Ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama kamar dab akin kwarya a wasu bangarori na jahohin Kano da Kwara da Niger a yau Juma’a da kuma ranar Asabar, Yayin da kuma za’a samu matsakaicin ruwan sama a wasu jahohin kasar nan guda 20.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin rahoton hasashen yanayi da hukumar ta fitar a ranar Alhamis.
Rahoton ya baiyana cewar, za’a iya fuskantar mamakon ruwan sama a cikin sa’oi 24, sannan kuma wasu wuraren za’a samu matsakaicin ruwan sama, yayin da za’a iya fuskantar tumbatsar koguna da zaizayar kasa, da kadawar iska mai karfi da Cida da kuma tsawa.
Hukumar kula da yanayin ta kasa ta baiyana cewar jahohin da za’a iya fuskantar matsakaicin ruwan sama a gobe Asabar, sun hada da wasu bangarori na jihar Ribas sai Delta da Bayelsa da AKwa Ibom da Cross River da Yobe.
Sauran sune Benue da Jigawa da Katsina sai Zamfara da kuma jahar Sokoto.