Hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandire ta yammacin Afrika, WAEC, Ta ce za’a fara rubuta jarabawar kammala kammala makarantun sakandire ta SSCE daga ranar Litinin mai zuwa 8 ga watan da muke ciki zuwa ranar 23 ga watan Yunin bana a Najeriya.
Da yake yiwa manema Labarai karin haske, Shugaban Ofishin hukumar a nan Najeriya, Patrick Areghan, Ya baiyana cewar mutane Milyan 1 da dubu 621 da 853 daga makarantun sakandire dubu 20 da 851 zasu rubuta jarabawar a bana.
Ya kuma kara da cewar Daliban zasu rubuta jarabawar ne akan darussa daban daban har 76, A yayin da kwararrun manyan malaman makarantun sakandire dubu 30, zasu yi aikin saka ido a lokacin rubuta jarabawar ta SSCE.
Daga nan sai ya gargadi makarantu da su guji kin dora makin jarabawar gwaji ta daliban da zasu rubuta jarabawar akan lokacin da aka tsara.