Gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin fara bada lamunin karatu ga dalibai tsakanin watan Satumba da Oktoba n shekarar da muke ciki ta 2023.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya David Adejo ne ya bayyana hakan yau a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai akan kudirin dokar da shugaba Bola Tinubu ya sanyawa hannu.
Kudirin bada lamuni ga daliban da shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila ya dauki nauyi, ya tanadi bada rance marasa ruwa ga daliban Najeriya marasa galihu.
Adejo ya ce dokar za ta ba’wa ‘yan Najeriya talakawa damar zuwa manyan makarantu cikin sauki ta hanyar lamuni marar ruwa daga asusun bayar da lamuni na ilimi na Najeriya.