Gwamnatin tarayya ta ce za a fara amfani da Rigakafin zazzabin cizon sauro ta R21 a kasar nan nan da watan Afrilun 2024.
Ministan lafiya, Dr . Osagie Ehanire shi ne ya bayyana haka a jiya yayin wani taron manema labarai da aka shirya a Abuja, a wani bangare na ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya.
Ministan wanda babban sakataren ma’aikatar, Mamman Mamuda ya wakilta ya ce Najeriya ta nemi samun rigakafin har sau ukku a jere.
Ya ce ma’aikatar tana aiki kafada da kafada da hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tsara dabarun rarraba rigakafin zazzabin cizon sauro.