Jami’ar Bayero dake Kano ta sanar da dawowa cigaba da harkokinta na koyo da koyarwa makonni bayan da jami’ar ta tafi hutu saboda zabukan 2023.
Majalisar kolin Jami’ar ta ce ta gudanar da taronta na 402 a ranar Litinin inda ta yanke shawarar cewa za a ci gaba da gudanar da harkokin koyo da koyarwa daga yau Talata 21 ga watan Maris na shekarar 2023.
Majalisar Kolin Jami’ar ta Bayero ta amince da daidaita kalandar karatu ta 2022 da 2023 bayan hutun zabe.
Saboda haka ta bukaci daliban dake karatun digiri na biyu da kuma na masu karatu a makarantar harkokin kasuwanci ta Dangote da su duba cikakkun bayanai na sabuwar kalandar dake cikin mujallar jami’ar ta Bayero.