Kudirin dokar bada lamunin karatu ka daliban manyan makarantun kasar nan, da shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba ma hannu a jiya, Ta yi tanadin daurin shekara biyu ko biyan tarar naira dubu 500 ko kuma kuma a hadawa mutum duka,ga duk Dalibin da aka samu da lefin kin biyan bashin ko kuma saka wani yaki maida rancen da aka bashi.
Kazalika itama, kungiyar Dalibai ta kasa, taga baiken hanyoyin da aka dauka kan yadda za’a biya bashin ga daliban da suka karbi bashin.
Dokar dai ta bada damar kafa wani asusun ilimi na kasa, wanda zai kasance mai iko tafiyar da harkokin bada bashin karatun ga dalibai a kasar nan.
Asusun zai rika karbar takardun neman samun bashin ta hannun manyan makarantun da Daliban ke karatu a cikinsu.