Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Ya amince da daukar sabbin Malaman Makaranta Dubu 10 , wadanda zasu yi aiki a karkashin Hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar.
Wata sanarwa da shugaban Hukumar, Tijjani Abdullahi ya fitar, Yace tuni hukumar ta bawa Jami’ar jihar Kaduna damar tsara manhajar internet da za’a yi amfani da ita wajen daukar bayanan masu neman aikin, inda shafin zai fara aiki daga ranar 21 ga watan da muke ciki.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar Kaduna, Yace wadanda suka cancanci su nemi aikin koyarwar sune, masu shaidar takardar Malanta ta NCE ko kuma digiri a bangaren ilimi da suka fito daga makarantun da aka tabbatar da ingancinsu.
Ya kara da cewa wadanda suka cike bayanan nasu, zasu je dauke da takardunsu na ainihi domin tantancewa, sannan kuma daga bisani wadanda suka samu nasara, hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar zata wallafa sunayensu .