Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za a ci gaba da yin rijistar masu kada kuri'a sannan za'a bayyana sabuwar ranar rufe rijistar nan ba da dadewa ba.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Kwamishinan Zabe na Kano, Farfesa Riskuwa Arabu Shehu, ya ce an shirya tura karin na'urori 30 da ma’aikata domin cigaba da gudanar da aikin rijistar.
Kwamishinan ya bayyana damuwa akan kwararar masu yin rajista sau biyu a cibiyoyin hukumar ta INEC.
Sai dai Shehu ya bayyana cewa a yanzu haka akwai tsofaffin katinnan zabe guda dubu dari uku da tamanin da ba a karba ba.
Ya kuma ce sabbin Katin zabe dubu 77 da 117 na wadanda suka yi rajista daga watan Yuni zuwa Disamba 2021 suma suna nan ba a karba ba.