Kotun koli a Najeriya ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500, N1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Kotun kolin ta kuma soke tsarin gwamnatin tarayya na sake fasalin Naira, inda ta bayyana hakan a matsayin tsaran tsaye ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Kotun koli ta yanke hukunci a karar da aka shigar da gwamnatin tarayya kan sake fasalin Naira.
Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin da aka yanke, ya ce an yi watsi da korafin farko da Atoni Janar na Tarayya da gwamnatocin Bayelsa da Edo suka yi saboda kotun na da hurumin sauraron karar.
Ya kawo misali da sashe na 23 (2) na kundin tsarin mulkin kasa, kotun ta ce dole ne a shigar da matakan doka ko hujjoji wajen warware takaddamar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da jahohi.
Kotun kolin ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ya ke jawabi ga 'yan kasa ya amince cewa tsarin sauya fasalin na cike da matsaloli da dama.