Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da sake bude cibiyoyin koyon sana’oin dogaro da kai guda 26 da gwamnatin data gabata ta rufe su.
Kwamishinan aiyuka da gidaje na jihar Kano, Alhaji Marwan Ahmad, Ya baiyana cewar an samar da cibiyoyin ne a zamanin tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ganin mata da matasa sun koyi sana’oi daban daban.
Ya kara da cewar cibiyoyin zasu taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar shaye-shaye da sata a jihar nan.
Ya kuma baiyana cewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci ‘yan kwangilar da suke aikin shimfida titi mai tsawon kilomita biyar a daukacin kananan hukumomin jihar Kano, da su dawo bakin aikinsu batare da bata lokaci ba.
Hakazalika ya ce an dawo ci gaba da aikin ruwan Jakara dake cikin birnin kano wanda shima tsohuwar gwamnati ta yi fatali da shi.