On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Za'a Baza Jami'an Hukumar Kare Afkuwar Hadurra Ta Kasa Masu Makale Da Kyamara Dubu Daya A Shekara Mai Zuwa

JAMI'AN hUKUMAR KARE AFKUWAR HADURRA TA KASA

Hukumar Kare afkuwar Hadurra ta kasa, tace tana shirin baza jami’anta kimanin dubu 1 masu dauke da kyamarori a jikinsu zuwa sassa daban daban na kasar nan, a matsayin wata hanya ta bankado masu aikata rashin Da’a da karbar rashawa da kuma tattara bayanan wadanda aka cafke a cikin watanni 12 masu zuwa.

Kakakin hukumar, Bisi Kazeem ne ya tabbatar da haka a ranar juma’a, Yace  tuni jami’an hukumar 200 da aka fara bawa horo kan yin amfani da kyamarar wadda take makale a jikinsu, suka bazu zuwa bangarori daban daban na kasar nan, tun bayan kaddamar da tsarin a karkashin tsohon shugaban hukumar Boboye Oyeyemi a bara.

Yace a yanzu haka ana kan aikin horas da jami’an kare afkuwar hadduran ta kasa Dubu Daya, kan yadda zasu rika amfani da kyamarar, sannan kuma za’a rarraba su zuwa bangarori daban daban da zarar sun kammala daukar horo.

Idan ba’a manta ba a cikin watan Oktoban bara ne, Aka kaddamar da sabuwar fasahar a Abuja, karkashin tsohon shugaban hukuamr Oyeyemi, a wani mataki na bibiyar yadda  jami’an hukumar ke gabatar da aiyukansu.