Yawan mutanen da suka mutu a harin bam da sojoji suka kai Kaduna zuwa ranar Laraba ya kai 127, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.
Wani Limamin garin Tudun Biri, Alhaji Ahmed Sanusi, ya ce a kalla mutane 100 ne aka binne kwanaki uku da suka wuce, yayin da tawagar binciken ta gano tare da binne gawarwaki 20 a ranar Talata.
Ya kara da cewa, ya zuwa ranar Laraba an sake gano wasu gawarwaki shida tare da binne su, yayin da wani kuma ya mutu a asibitin koyarwa na Barau Dikko, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 127.