On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yawan Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Cutar Mashako A Jihar Kano Sun Kai 100

Mashako

Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Mashako a jihar Kano ya kai 100.

Alkaluman bayanan  da Cibiyar  dakile  yaduwar  Cututtuka ta  kasa, NCDC ta fitar a ranar 30 ga  watan  Yulin da  ya  gabata, ya sha  banban  da adadin mutanen da suka mutu  saboda  cutar  su guda  76  da aka  samu a watan  Yunin bana.

Sabbin bayanan na  zuwa ne a  yayin da   gwamnatin jihar  kano  ta ce tana bukatar alluran rigakafin da bai gaza miliyan shida ba domin yaki  da bazuwar  cutar  ta Mashako.

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan wadanda suka kamu da cutar Mashako a kasar nan,  inda mutane  dubu  1  da  207 aka tabbatar da sun kamu da cutar  daga cikin mutane dubu   3  da 234  da aka yiwa  gwajin cutar  ta Mashako.