A yanzu haka yawan mutanen da suka harbu da Cutar Kyandar Biri a kasar nan sun kai 141 a maimakon 110 da aka samu a lokacin baya, kamar yadda cibiyar Dakile yaduwar Cututtuka ta kasa ta baiyana.
Cibiyar ta baiyana haka ne ta cikin wani sabon rahoton data wallafa kan halin da ake ciki game da cutar Kyandar Biri, Yace daga ranar 6 zuwa 12 ga watan da muke ciki, an samu sabbin mutane 31 da suka harbu da cutar a jihohi 13.
Jihohin sun hada da Legas mai 5 sai Katsina da Ondo da Bayelsa masu hurhudu kowannensu, Yayin da Nasarawa keda 3 sai ogun itama mai 3 Yayin da Oyo keda 2, Sai kuma jihohin Akwa ibom da Delta da Edo da jihar Kaduna da Nan Kano da kuma Imo masu dai-dai.