On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Yawan Mutane Da Suka Mutu Sanadiyar Cutar Mashako Sun Karu Zuwa 32 A Jihar Kano - NCDC

Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a kasarnan NCDC ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu sanadiyar cutar mashako sun  haura 32 a jihar Kano.

Darakta Janar na hukumar NCDC, Dr Ifedayo Adetifa, shine ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake zantawa da jaridar Punch, inda yace adadin wadanda aka tabbatar sun kamu ya karu zuwa 123 a kasarnan.

Adetifa yace sakamakon binciken da aka yi ya nuna cewa jihar Kano ta samu mutum 100 da aka tabbatar sun kamu da cutar inda 32 suka mutu, sai kuma jihar Yobe mai mutane 17 sun kamu sannan aka tabbatar da mutuwar uku.

Ya kara da cewa jihar Legas ta samu mutum biyar da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan uku sun mutu, yayin da jihar Osun ta samu mutum daya.

Ya bukaci iyaye da su tabbatar an yiwa ‘ya’yansu allurar rigakafin kamuwa da cutar.

Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku ne kawai a ranar Asabar din da ta gabata alkaluman da sukaci karo da bayanan farko da kuma kididdigar NCDC.