On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Yawan Busussukan Da Najeriya Zata Biya Na Shekarar 2022 Ya Karu - DMO

Yawan basussukan da Najeriya zata biya ya karu da kashi 14.68 zuwa Naira trilliyan 3.36 a shekarar 2022 kamar yadda bayanai daga Ofishin kula da basusska na kasa ya nuna.

A cewar offishin, an kashe Naira triliyan 2.93 wajen biyan basussukan kasashen waje da na cikin gida a shekarar 2021.

Wani bincike da offishin busussuka ya gudanar ya nuna cewa kasar ta kashe dala biliyan 2.4 wanda ya yi daidai da Naira tiriliyan 1.07 ta amfani da kudin canjin dalar Amurka 460 a halin yanzu wajen biyan basussukan kasashen  waje a shekarar bara.

Biyan bashin cikin gida ya lakume Naira trilliyan 2.56 a shekarar 2022, inda aka kashe mafi yawa na Naira biliyan 529.88 a watan Afrilu.