Ofishin kula da basussuka na Najeriya ya ce jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira trilliyan 87.38 a karshen zango na biyu na shekarar 2023.
Adadin ya nuna karuwar kashi 75.29 ko kuma Naira trilliyan 37.53 idan aka kwatanta da Naira trilliyan 49.85tn da aka samu a karshen watan Maris na 2023.
Ofishin a wani rahoto da ya fitar a ranar Alhamis ya ce bashin ya hada dana babban bankin Najeriya da yake cigaba da baiwa gwamnatin tarayya Na triliya 22.71.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, sauran kari a kan basussukan, wasu sabbin rance ne na gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi daga gida da waje.