Yawan bashin da ake bin Najeriya a Kasashen waje zai kai sama da dala biliyan 51 da milyan 759, yayin da a jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dokoki ta kasa, domin karbo sabon lamunin dala biliyan 8 da milyan 6 da kuma Euro miliyan 100 daga kasashen waje.
Bukatar Shugaban kasar wani bangare ne na basussukan da za’a ciwa daga kasashen daga shekarar 2022 zuwa 2024 domin gudanar da muhimman aiyukan raya kasa, kamar wutar lantarki da samar da hanyoyi da inganta samar ruwa da shimfida layin dogo da kuma bunkasa fannin kiwon lafiya.
A cewar ofishin kula da ciwo basussuka na kasa, yawan bashin da ake bin kasar nan zuwa watan Yunin da ya gabata, ya kai dala biliyan 43 da milyan 159, yayin da bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 54 da bilyan 130.
Zuwa yanzu jimillar bashin da ake bin Najeriya na cikin gida da kasashen waje ya kai Naira tiriliyan 87 da bilyan 379.