Hukumar kula da harkokin man fetur ta ta kasa ta ce yawan man fetur da Najeriya ke amfani da shi a kullum ya ragu zuwa lita miliyan 46 da dubu 38, sakamakon cire tallafi.
Shugaban hukumar, Ahmed Farouk, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da masu gudanar da harkokin man fetur da iskar gas a ranar Litinin a Legas, ya ce adadin ya nuna raguwar kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 a kowace rana, kafin a cire tallafin.
A cewarsa, matsakaicin man da ake sha a kullum ya ragu bayan sanar da cire tallafin a ranar 29 ga watan Mayu zuwa lita miliyan 46.38.
Dangane da shigo da mai, Farouk ya ce sama da kamfanoni 56 ne suka nemi lasisin shigo da mai, yayin da guda 10 kacal suka yi alkawarin shigo da man.