On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yaune Kotu Zata Baiyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan Kano A PDP

MOHAMMED SANI ABACHA DA SADIQ AMINU WALI

A yanzu haka ana cikin zaman zullumi a reshen jam’iyyar PDP ta nan jihar Kano kan abunda zai iya kasancewa, a yayin da a yau ne kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan wane ne halastaccen dan takarar gwamnan jihar kano, a karkashin jam’iyyar tsakanin Mohammed Sani Abacha da Kuma Sadiq Aminu Wali.

Idan  ba’a  manta  ba  a baya, wata  babbar  kotun taraiyya  ta  baiyana  zaben fidda  dan takarar  gwamnan jihar Kano a jam’iyyar  ta  PDP  da aka  gudanar  a  Lugard, wanda  Mohammed  Abacha  ya samu nasara  a matsayin halastacce, a  yayin da  ta  yi fatali  da zaben  fidda  gwani na jam’iyyar  da aka yi a cibiyar  koyar da  matasa  sana’oi  ta  Sani Abacha  dake nan Kano.

Sai  dai  saboda  rashin amincewa  da yadda  hukuncin ya kasance, Sadiq  Aminu Wali wanda  ya kasance  dan tsohon ministan harkokin wajen kasar nan, Aminu Wali  ya garzaya  kotun daukaka  kara, inda  yake  neman ta bi masa  hakkinsa.